Featured
Gwamnati ta rufe Cocina 3 kan damun Jama’a da kara yayin gudanar da Ibadunsu
Gwamnatin Jihar Ogun ta rufe wasu coci-coci guda uku saboda suna damun jama’ar yankunansu da kara.
Da yake rufe cocinan a birnin Ibadan, mashawarcin gwamnan jihar kan muhalli, Farook Akintunde, ya ce an sha gargadin aike wa cocinan takardar gargadi da kuma zaman tattaunawa da cewa su daina hana jama’a sakat amma suka ki.
Akintunde ya ce an samu cocin Christ Apostolic da ke yankin Gbogunmi yana amfani da manyan sifiku a lokacin ibadar yamma da na tsakar dare, wanda karar sifikun ke hana jama’ar unguwar sukuni.
Ina So In Amsa Gayyatar Kotu Amma Ina Tsoron Kar A Kama Ni – Yahaya Bello
“Duk kokarinmu na ganin shugabannin cocin sun kiyaye lamarin ya ci tura, amma babu gwamnatin da za ta zura ido ana cutar da lafiyar al’ummar da take shugabanta,” in ji Akintunde.
Daga nan ya yi gargadin cewa wuraren ibada su daina damun jama’a da kara, saboda gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa wajen rufe duk wanda ya saba dokar ba.
