Featured
Gwamnati Ta Dakatar Da Harajin Kashi 15% Na Shigo Da Man Fetur Da Dizal
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin aiwatar da harajin kashi 15 cikin 100 kan man fetur da dizal da ake shigo da su daga ƙasashen waje. Hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa (NMDPRA) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce aiwatar da wannan haraji “ba ya cikin tsare-tsare a halin yanzu.”
A baya, rahotanni sun nuna cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da shigar da wannan haraji mai suna ad-valorem a kan man fetur (PMS) da dizal (AGO). Sai dai NMDPRA ta ce an janye wannan mataki ne domin kauce wa matsalolin farashi da karancin man da hakan zai iya jawo wa.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa akwai wadataccen man fetur, dizal da iskar gas a ƙasar, waɗanda ke fitowa daga matatun gida da kuma shigo da su daga waje, domin tabbatar da ci gaba da wadatar man a tashoshin a lokacin da ake bukata sosai.
Ta roƙi ’yan kasuwa da masu tashoshi da su guji boye mai ko ƙara farashi ba bisa ka’ida ba, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da sa ido kan harkar rarraba mai don kaucewa kowace irin tangarda. NMDPRA ta kuma tabbatar da aniyar ta wajen tabbatar da tsaron makamashi da wadatar mai a fadin ƙasar.
