Featured
Motocin Agaji Sun Fara Shiga Gaza Bayan Isra’ila Ta Amince
Manyan motoci ɗauke da kayan agaji sun tsallaka Gaza daga Masar bayan samun izini daga Isra’ila.
Isra’ilar ta ce ta tsagaita wuta ta ɗan lokaci a wasu sassan Gaza domin bayar da damar shigar da kayayyakin abinci da magani, waɗanda ta hana tsawon watanni.
Matakin na zuwa ne yayin da ma’aikatar lafiya a Gazan ta ce ƙarin mutum shida sun mutu saboda yunwa cikin awa 24 da suka gabata.
Shugaban hukumar ba da agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya Tom Fletcher ya yi maraba da dakatar da buɗe wutar, yana mai cewa yana magana da ma’aikatan da ke gudanar da aikin raba kayan.
