Connect with us

Featured

Majalisar Dattawa Ta Baiwa NNPCL Mako Uku Ya Kare Kansa Kan Ɓatan Tirilyan 210

Kwamitin Majalisar Dattawa na bin Diddigi ya ba Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) wa’adin mako uku ya amsa tambayoyi kan rashin ba da ba’asi kan Naira tiriliyan 210 da ba a san inda suka shiga ba daga shekarar 2017 zuwa 2023.

An dai bayar da wa’adin ne ga shugaban kamfanin na kasa, Bayo Ojulari, wanda ya bayyana a gaban kwamitin ranar Talata 29 ga Yuli, bayan ya bayar da hakuri kan rashin bayyanarsa yayin gayyatar da kwamitin ya yi masa a baya.

Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin Ahmed Wadada Aliyu (Nasarawa), ya tsaya kai da fata cewa dole kamfanin ya bayyana inda kudaden suka shiga.

Ojulari dai ya ba kwamitin hakuri, inda ya ce yana bukatar karin lokaci kafin ya iya amsa tuhuma 19 da ake yi masa.

Ya kuma ce, “Da kadan na haura kwana 100 a matsayin shugaban wannan kamfanin. Ina bukatar karin lokaci kafin na iya zakulo bayanan da kuka bukata. Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da sauran tarin ayyuka ke jira na.

“Ni kaina ina bukatar fahimtar abubuwan da kaina kafin na iya bayar da amsa a kansu. Amma zan je na zauna da sauran ma’aikatana da suka dace mu tattauna domin bayar da abin da ake bukata,” in ji shugaban na NNPCL.

Kodayake mako hudu ya bukata, amma kwamitin ya ba shi mako uku ne domin ya gabatar da bayanan.

Da yake karin haske a kan kudaden, Sanata Wadada ya ce kudaden da ake magana a kansu kashi biyu ne, akwai Naira tiriliyan 103 da kuma Naira tiriliyan 107 su ne ake bukatar bayanan a kan su.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet