Featured
Malaman Jinya Sun Tsunduma Yajin Aiki A Najeriya
A yau Laraba 30 ga Yuli 2025, an fara yajin aikin da zai iya kawo cikas ga ayyukan lafiya a fadin Najeriya, yayin da mambobin kungiyar National Association of Nigeria Nurses and Midwives (NANNM) daga manyan asibitocin gwamnatin tarayya, suka fara yajin aikin gargadi na kwana bakwai.
Yajin aikin ya fara ne da misalin karfe 12 na dare bayan karewar wa’adin kwana 15 da kungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya domin magance matsalolinsu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama tsakanin likitoci da gwamnati dangane da batun walwala da sauran matsaloli.
Da yake magana da Daily Trust a ranar Litinin, Shugaban NANNM reshen manyan cibiyoyin lafiya na tarayya, Comrade Morakinyo Rilwan, ya ce yajin aikin zai shafi duka ayyukan jinya a manyan asibitocin gwamnati.
“Wa’adin kwana 15 ya kare da karfe 12 na dare ranar Talata, 29 ga Yuli, 2025. Yajin aikin zai fara ne da misalin 12:01 na safiyar Laraba, 30 ga Yuli, 2025.”
Yajin aikin ya shafi asibitoci 74 na gwamnati, wadanda suka hada da manyan asibitocin koyarwa, cibiyoyin lafiya na tarayya, asibitocin kwararru irin su na kashi, kwakwalwa da ido, da kuma dukkan asibitocin gwamnati a fadin jihohi 36 na Najeriya da Babban Birnin Tarayya, har da asibitoci a kananan hukumomi 774.
Ya bayyana cewa asibitocin masu zaman kansu ba su cikin yajin aikin, saboda babu wadatattun nas na zaman kansu da suka yadu a duk fadin kasa.
Rilwan ya ce dalilan yajin aikin sun hada da:
Karancin albashi,
Rashin isassun ma’aikata,
Rashin biyan wasu hakkokin kudi,
Da kuma yanayin aiki da ke cike da hadari ga lafiyar ma’aikata.
A ranar 14 ga Yuli, 2025, kungiyar ta fitar da wa’adin kwanaki 15 ga gwamnatin tarayya tana neman ta dauki mataki domin kaucewa durkushewar bangaren lafiya baki daya.
Sai dai ya ce har zuwa karewar wa’adin, gwamnatin tarayya da ma’aikatar lafiya ba su tuntubi kungiyar ba, kuma hakan ya tilasta su shiga yajin aikin.
“Tun da muka fitar da wa’adi a ranar 14 ga Yuli, babu wani gayyata daga gwamnati ko ma’aikatar lafiya. Saboda haka, ba makawa yajin aikin zai gudana – kuma zai shafi duka cibiyoyin lafiya na gwamnati a matakin tarayya, jiha da kananan hukumomi,” in ji shi.
Ya kara da cewa matakin na yajin aikin na da nufin janyo hankalin gwamnati kan matsalolin da ke addabar nas a fadin kasar.
“Wannan yajin aiki na biyo bayan wa’adin da muka bai wa gwamnatin tarayya ne ta hannun ma’aikatar lafiya a ranar 14 ga Yuli, 2025, saboda kokarin da muka yi na neman a biya bukatunmu ya ci tura,” a cewar sa.
