Connect with us

Featured

Amnesty International Ta Yi Alla-wadai Da Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM a Jihar Neja

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya, Amnesty International, ta yi Allah-wadai da umarnin da Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya bayar na rufe gidan rediyo Badeggi 90.1 FM da ke Minna.

A wata sanarwa da Shugaban Amnesty International na Najeriya, Isa Sanusi, ya fitar a ranar Asabar 02 ga Agusta, kungiyar ta bayyana cewa zargin da aka yi wa gidan rediyon na “tayar da hankali” da kuma umarnin da aka bayar na janye lasisin gidan rediyon tamkar cin zarafi ne da amfani da iko ba bisa ka’ida ba.

Sanusi ya ce wannan umarni da gwamnan ya bayar ba shi da tushe balle makama, musamman duba da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a jihar – har da kashe-kashe da korar jama’a daga gidajensu da ‘yan bindiga ke yi.

Ya ce: “Amnesty International na Allah-wadai da wannan umarni na rashin adalchi, tare da saɓa doka da kuma danniya da Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bayar na rufe gidan rediyon Badeggi 90.1 FM – wanda shi ne daya daga cikin hanyoyin yada labarai masu zaman kansu ga al’ummar jihar.”

Ya kara da cewa: “Zargin da gwamnan ya yi na cewa gidan rediyon na ‘tayar da hankali’ da umarnin da ya bayar na a janye lasis dinsa, abu ne da ke nuna amfani da iko ba bisa ka’ida ba da rashin amincewa da ra’ayoyi masu sukar gwamnati.”

Sanusi ya bukaci gwamna Bago da ya janye umarnin rufe gidan rediyon nan da nan, yana mai jaddada cewa gwamna ba shi da ikon rufe gidan watsa shirye-shirye bisa dokar Najeriya.

Tun a ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamna Umar Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM a yayin wani taron jam’iyyar APC da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Minna.

Ya ce wannan matakin ya zama dole ne saboda a cewarsa, ayyukan gidan rediyon na sabawa ka’idojin aikin jarida.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet