Featured
Ambaliya Ta Shafi Mutane 119, 791 Yayin Da Mutane 165 Su Ka Rasa Ransu a 2025 – NEMA
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa akalla mutane 165 ne suka rasa rayukansu, 82 su ka ɓace, yayin da ambaliya ta shafi mutane 119,791 a bana.
NEMA ta bayyana hakan ne a cikin bayanan kididdigar da ta wallafa a dandalinta na yanar gizo a ranar Juma’a 01 ga Agusta, 2025.
Hukumar ta ƙara da cewa mutane 138 sun jikkata da raunuka iri-iri, 43,936 aka raba su da muhallansu, gidaje 8,594 ambaliya ta shafa, da gonaki 8,278 da aka lalata a cikin ƙananan hukumomi 43 da ke jihohi 19.
A cewar hukumar, yara da mata su ne suka fi fuskantar illar ambaliyar.
Ta ce: “Yara 53,314, mata 36,573, maza 24,600, tsofaffi 5,304 da kuma nakasassu 1,863 ne suka fi shan wahala a wannan ambaliya ta bana.”
Jihohin da suka fi yawan waɗanda abin ya shafa sun haɗa da: Imo, Rivers, Abia, Borno da Kaduna.
Ga jerin jihohi 19 da ambaliyar ta shafa: Abia, Babban Birnin Tarayya (FCT), Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Neja, Ondo, Rivers da Sokoto.
