Featured
Mutane 41 Aka Ceto Yayin Da 4 Su Ka Rasu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Sokoto – NEMA
Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ce an ceto mutane 41 yayin da mutane 4 suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya auku a Goronyo, jihar Sokoto. Wannan na cikin wata sanarwa da aka fitar ranar juma’a, 22 ga Agusta, 2025, dauke da sa hannun shugaban sashen yada labarai na nema, manzo ezekiel.
A cewar sanarwar, karin gawa daya aka tono a safiyar juma’a wanda ya sa adadin wadanda suka mutu ya tashi zuwa hudu. An gudanar da sallar jana’iza bisa tsarin addinin musulunci, sannan aka binne shi nan take.
Hakanan, a ci gaba da aikin ceto ranar alhamis 21 ga watan Agusta, tawagar agaji ta kai ziyara garuruwan takuske, kwakwazu, bari da gamiha domin tantance wadanda suka bace da kuma jajantawa iyalan da suka yi rashi. A nan ne aka tabbatar da cewa mutane 16 sun tsira daga hatsarin.
Sanarwar ta kara da cewa an kammala aikin hadin gwiwa tsakanin nema, sema na sokoto, hukumar ruwa ta kasa (niwa), karamar hukumar goronyo da kuma masu nutsewa na al’umma. Darakta janar na nema, hajiya zubaida umar, ta yabawa jajircewar tawagar da kuma kokarin duk masu ruwa da tsaki.
