Connect with us

Featured

Ba Zan Taɓa Bawa Ɗana Shawarar Ya Bugawa Najeriya Wasa Ba – Taribo West

Tsohon ɗan wasan bayan Super Eagles, Taribo West, ya caccaki Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) da kuma Gwamnatin Jihar Legas saboda abin da ya kira watsi da iyalin marigayi Peter Rufai, tsohon mai tsaron ragar ƙasar. Ya bayyana haka ne ranar Juma’a 22 ga Agusta, a wurin jana’izar Rufai a Legas, inda ya nuna takaicinsa kan yadda ake mantawa da jaruman kwallon ƙafa bayan rasuwarsu.

Taribo, wanda ya taba bugawa Inter Milan, ya bayyana cewa lamarin ya yi matuƙar daga masa hankali, inda ya tuna irin irin rawar da Rufai ya taka wa ƙasar. Ya ce abin bakin ciki ne ace gwamnati da NFF sun watsar da nauyin da ya rataya a wuyansu ga iyalin marigayin, lamarin da ya kira rashin adalci ga masu sadaukar da rayuwarsu don ƙasar.

Ya kuma tuna irin wannan watsi da aka yi wa manyan tsoffin ’yan wasa irin su Stephen Keshi, Rashidi Yekini, da Thompson Oliha. West ya ce hakan ne ma yasa bai taɓa tunanin ba wa ɗansa shawarar ya buga wa Najeriya wasa ba, saboda rashin mutunta waɗanda suka yi hidima ga ƙasar bayan sun bar duniya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet