Connect with us

Featured

Yawaitar Kafa Jami’o’i Zai Rage Martabar Digiri A Najeriya – ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana rashin jin daɗinta kan amincewar da Gwamnatin Tarayya ta yi, na kafa sababbin jami’o’in masu zaman kansu duk da cewa gwamnatin ta sanar da dakatar da hakan na tsawon shekara bakwai. Sanarwar ta fito daga shugaban ƙungiyar, Farfesa Christopher Piwuna, a ranar Alhamis 21 ga Agusta, 2025 a Abuja. Ya ce kafa sababbin jami’o’i a wannan lokaci bashida wata ma’ana.

ASUU ta yi nuni da cewa Najeriya na da jami’o’i 339, ciki har da na tarayya 72, na jihohi 108, da na kashin kai 159. Ta ce wannan adadi ya wadatar, kuma abin da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali a kai shi ne inganta waɗanda ake da su. Ƙungiyar ta gargadi cewa yawaitar kafa jami’o’i zai ƙara lalata darajar ilimi da rage martabar digiri a ƙasar.

Ƙungiyar ta kuma bayyana damuwa kan yadda mafi yawan jami’o’in gwamnati ke fama da ƙarancin ɗalibai duk da adadin ma’aikatan da suke da su. Ta ce wannan matsala tana nuna yadda ake raba albarkatu ba tare da tsari ba, abin da ke haifar da asara ga kuɗaɗen gwamnati. ASUU ta zargi gwamnatoci da amfani da lasisin kafa jami’a a matsayin siyasa.

A ƙarshe, ASUU ta sake jaddada bukatunta da suka haɗa da sabunta yarjejeniyar 2009, bayar da kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i, da biyan bashin albashi da matsayi na malaman jami’a. Ta ce dole gwamnati ta daina kafa sababbin jami’o’in da ba ta da shirin bunƙasa su. Ƙungiyar ta yi gargadin cewa gazawa wajen yin haka zai ci gaba da kawar da jami’o’in Najeriya daga jerin manyan jami’o’i a duniya.

 

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet