Connect with us

Featured

ASUU na shirin tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta yi barazanar sake fara yajin aikin ƙasa baki ɗaya, idan gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi ba su gaggauta magance matsalolin da suka shafi malaman jami’o’i ba.

ASUU ta ce za ta iya dawo da yajin aikin “ba tare da ƙarin sanarwa ba”, saboda rashin cika yarjejeniyar da aka cimma a Disamba 2025, da kuma rashin biyan sauran watanni 3.5 cikin albashin da aka riƙe. Ƙungiyar ta kuma ce ba a tura wasu kuɗaɗen fansho da sauran cire-cire daga albashin malamai da suka kai biliyoyin naira ba.

Read Also : NDC za ta nemi gudummawar kuɗi daga ƴan Najeriya domin gudanar da yaƙin neman zaɓe

Shugaban ASUU, Christopher Piwuna, ya ce wasu jihohi ciki har da Abia, Bauchi, Ekiti, Ogun, Benue, Yobe, Adamawa, Kebbi, Katsina da Borno sun fara aiwatar da yarjejeniyar. Ya ce Kano, Edo, Plateau, Taraba, Gombe da Bayelsa ma sun yi alƙawarin fara aiwatar da ita a Satumba ko Oktoba.

ASUU ta ce rashin cika yarjejeniyar 2025 da kuma rashin biyan kuɗaɗen da ake bin malamai na barazana ga zaman lafiyar jami’o’in ƙasar. Ta buƙaci gwamnatin tarayya da jihohi su gaggauta ɗaukar mataki, tana mai cewa ba za ta ɗauki alhakin sakamakon da zai biyo bayan sake dawo da yajin aikin ba.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet