Connect with us

Featured

Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta kashe N522m wajen sayen bindigogi da alburusai amma ba’a san inda suke ba

Wani rahoton Binciken Kudi na Gwamnatin Tarayya ya ce Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya ta kashe Naira Miliyan 522,490,349 wajen sayen bindigogi da alburusai, amma ba a gabatar da hujjar karɓar kayayyakin ba. Rahoton ya ce an yi amfani da kudaden ne da nufin karfafa tsaron filayen jiragen saman Najeriya.

Rahoton ya ce ma’aikatar ta biya Naira Miliyan 270,020,066.80 a ranar 10 ga janairu da kuma 23 ga mayun 2023 domin sayen bindigogin ƙirar AK, da alburusai da nufin karfafa tsaron filayen jiragen saman Nijeriya. Sai dai babu amincewar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) da aka gabatar, sannan babu wasu takardun da suka dace da tsarin biyan kudin da aka haɗa, ciki har da takardar da ke nuna cewa an karɓai kayayyakin.

Read Also : ASUU na shirin tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya

Haka kuma, an biya ƙarin N252,470,282.20 domin sayen Sub-Machine Guns, Pistols da alburusai. Ma’aikatar ta ce an bi dukkan matakan saye tare da samun takardun amincewa da suka dace, ciki har da izinin ofishin NSA da sauran takardun kwangila, amma Auditor-General ya ce bayanin ma’aikatar bai gamsar da shi ba, kuma binciken nasa ya ci gaba da nanata wannan matsala.

Rahoton ya kuma ce ma’aikatar ta biya N163,918,943.69 ga ’yan kwangila shida domin aikin gina hasumiyoyin kula da jiragen sama a filayen jiragen sama shida. An ce wasu daga cikin kwangilolin an aiwatar da su ta hanyar wakilai, kuma babu hujjar aikin da aka yi kan kudin da aka biya, lamarin da rahoton ya ce zai iya jefa gwamnati cikin haɗarin asarar kuɗi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet