Connect with us

Featured

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Dakatar Da Ziyarar Aiki Zuwa Afirka Ta Kudu

Majalisar Dokokin Najeriya ta dakatar da dukkan ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu, tare da umartar ’yan majalisa da jami’anta da su kaurace wa duk wasu ayyukan majalisa da hukumomin Afirka ta Kudu suka shirya ko suka dauki nauyin gudanarwa har sai an sake duba matakin. Kakakin Majalisar Wakilai, Akin Rotimi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a 11 ga Satumba, 2026.

Matakin ya biyo bayan rahotannin ci gaba da kai hare-haren kyamar baki, tashin hankali, tsoratarwa da lalata kadarorin ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka da ke zaune a Afirka ta Kudu. Majalisar ta ce ta damu musamman da rahotannin kashewa, raunatawa da korar wasu ’yan Najeriya daga wuraren kasuwancinsu, gidajensu da sauran kadarorinsu.

Read Also : Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta kashe N522m wajen sayen bindigogi da alburusai amma ba’a san inda suke ba

Umarnin ya shafi ziyarar ’yan majalisa, kwamitoci, jami’ai da ma’aikatan Majalisar, da kuma tarurruka, tarukan karawa juna sani, bitoci da sauran hulɗar majalisa da hukumomin Afirka ta Kudu ke shiryawa. Dakatarwar ta shafi tarukan da ake gudanarwa a zahiri da kuma na yanar gizo, sai dai ana iya samun izini na musamman daga shugabancin Majalisar.

Majalisar ta ce dakatarwar ba tana nufin lalata dadaddiyar alakar diflomasiyya da zumuncin jama’a tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu ba. Ta ce har yanzu hulɗar majalisu na da muhimmanci, amma dole ne ta kasance bisa mutunta juna da kuma kudurin kare rayuka, dukiyoyi da harkokin kasuwanci na halal, yayin da dakatarwar za ta ci gaba har sai an sake ba da wani umarni.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet