Featured
An Yanke Wutar Lantarki a Ofishin Jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu
An yanke wutar lantarki a ofishin Jakadancin Najeriya dake birnin Tshwane, Afirka ta Kudu, sakamakon bashi da ake binsu kan kudin amfani da wutar.
Babban jami’in birnin, Dr Nasiphi Moya, ya bayyana a shafin X cewa an yanke wutar ne saboda ofishin Jakadancin bai biya kudin lantarkin da ya kamata ba. Sai dai, sa’o’i kadan bayan haka, Dr Moya ya sanar da cewa an dawo da wutar lantarkin.
Wannan ba shine karo na farko da bashin ya jawo yanke wuta a ofishin Jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu ba. A watan Janairu na 2023, kamfanin rarraba wutar lantarki na City Power ya yanke wutar ofishin Jakadancin Najeriya dake Johannesburg saboda bashin dala 35,000.
