Featured
Iran Za Ta Fara Tattaunawa da Amurka Kan Shirin Nukiliya
Shugaban majalisar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ya ba da umarnin ga ministan harkokin wajen ƙasar da ya fara tattaunawa da Amurka kan shirin nukiliyar Iran. Pezeshkian ya ce manufar tattaunawar ita ce neman hanyoyin da za a samar da maslaha ta “ba cuta, ba cutarwa.”
A gefe guda, Shugaban Amurka, Donald Trump, na ci gaba da barazanar sake kai hare-hare a Iran, inda ya yi gargadi cewa za su fi waɗanda aka yi a baya zafi idan Iran ta ci gaba da shirinta na nukiliya. Trump ya kuma zargi hukumomin Iran da amfani da karfi wajen murƙushe masu zanga-zanga, lamarin da Tehran ta musanta.
Ana sa ran ministan harkokin wajen Iran, Abbas Arapchi, zai gana da wakilin Trump na musamman a Gabas ta Tsakiya, Steve Wikoff, domin ci gaba da tattaunawar diplomasiya.
