Featured
Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Amurka Da Iran Ta Rushe – Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta rushe bayan sabbin hare-haren da ɓangarorin biyu suka kai wa juna. Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a taron ƙasashen NATO.
Trump ya ce ba ya da sha’awar ci gaba da mu’amala da Iran, yana mai bayyana tattaunawa da ƙasar a matsayin “ɓata lokaci.” Haka kuma, ya yi kalamai masu zafi kan shugabannin Iran, yana mai cewa ba ya ganin wata fa’ida a ci gaba da hulɗa da su.
Read Also : Za Mu Yi Amfani da Fasahar Zamani Wajen Yaƙi da Matsalar Tsaro – Tinubu
Kalaman Trump sun zo ne bayan Amurka da Iran sun yi musayar hare-hare tare da zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a baya, lamarin da ya sake tayar da hankalin rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
