Featured
Iran Ta Ba Wa Jirgin Turkiyya Izinin Wucewa Ta Mashigar Hormuz
Ministan sufurin ƙasar Turkiyya, Abdulkadir Uraloğlu, ya bayyana cewa Iran ta ba wani jirgin ruwan ƙasarsu izinin wucewa ta Strait of Hormuz. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa jirgin yana kusa da ruwan Iran a lokacin da aka ba shi izinin.
Uraloğlu ya ce gwamnatin Ankara ta ɗaga matakin gargaɗin zuwa mafi girma sakamakon halin da ake ciki a mashigar. Ya ƙara da cewa a halin yanzu akwai jiragen Turkiyya 14 da ke jiran izinin wucewa, yayin da gwamnatin ƙasar ke ci gaba da tattaunawa da jami’an Iran kan halin da jiragen ke ciki.
A makon da ya gabata, rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps ta sanar cewa ta karɓe ikon zirga-zirgar ruwa a mashigar a matsayin martani ga hare-haren da America da Israel suka kai Iran. Sabon jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei, ya kuma jaddada cewa mashigar za ta ci gaba da kasancewa a rufe.
