Featured
Mun Kai Hari Kan Cibiyoyin Nukiliyar Iran – Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ƙasarsa ta kai wasu hare-hare kan muhimman cibiyoyin nukiliya guda uku da ke cikin Iran.
A lokacin da yake jawabi a fadar White House a daren jiya Asabar21 ga Yuni, 2025. Ya ce hare-haren da za a kai nan gaba za su fi yawa kuma za su fi muni matukar Iran ba ta nemi sasanci ba.
“Mun tarwatsa duka muhimman cibiyoyin makamasin nukiliya na Iran, kuma yanzu ya zame mata dole ta nemi a yi sulhu don kawo karshen hare-haren,” in ji Trump.
Trump ya taya firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu murna, ya kuma ce sun yi aiki tare don kawar da abin da ya bayyana a matsayin mummunar barazana ga Isra’ila.
