Featured
Majalisar Dokoki Ta Buƙaci a Sauya Lokacin Zaɓen Shugaban Ƙasa
Majalisar Dokokin Najeriya ta ba da shawarar sauya lokacin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa daga watan Fabrairun 2027 zuwa Nuwamban 2026, domin bai wa kotuna isasshen lokaci su kammala shari’o’in zaɓe kafin rantsar da sabbin shugabanni.
Shawarar na cikin daftarin ƙudurin dokar zaɓe ta 2025 da aka gabatar a zaman sauraron ra’ayoyin jama’a da kwamitocin zaɓe na majalisun dokokin biyu suka gudanar a Abuja ranar Litinin.
Daftarin ya tanadi cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni akalla kwana 185 kafin ƙarshen wa’adin mulkin shugabannin da ke ofis, maimakon tsarin da ake amfani da shi a yanzu.
Ƴan majalisar sun bayyana cewa wannan sauyin zai taimaka wajen tabbatar da cewa an kammala dukkan ƙorafe-ƙorafen zaɓe kafin ranar 29 ga Mayu 2027, ranar rantsar da sabbin shugabanni, tare da rage cikas da rikice-rikicen shari’a bayan zaɓe.
