Connect with us

Featured

Zan Duba Yiwuwar Amincewa Da Kafa Ƙasar Falasɗinu- Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai yi nazari tare da yin shawara kan yadda ya ga ya dace game da yiwuwar amincewa da kafa Ƙasar Falasɗinu a matsayin hanyar samar da maslaha a yankin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya bayyana haka ne ga manema labarai yayin dawowarsa daga ziyarar da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya ranar Litinin, inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a Gaza. Ya ce zai yi aiki tare da sauran ƙasashen duniya don nemo mafita mai dorewa ga rikicin yankin.

Kasashe da dama na duniya sun dade suna kira da a amince da kafuwar ƙasar Falasɗinu, musamman a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a Amurka a kwanakin baya. Wannan matsin lamba na ƙasa da ƙasa yana ƙara ɗora alhakin matsaya kan gwamnatin Trump.

A ranar Litinin, yayin da Shugaba Trump ke gabatar da jawabi a majalisar dokokin Isra’ila, wani ɗan majalisa ya nemi ya bayyana matsayinsa kan kafuwar Falasɗinu. Wannan lamari ya janyo hankalin jami’an tsaro, inda suka fitar da ɗan majalisar daga zauren cikin gaggawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet