Featured
Na Yarda Ana Kashe Musulmai a Najeriya – Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa Musulmai ma na daga cikin wadanda ake kashewa a Najeriya, duk da cewa ya jaddada ikirarin cewa Kiristoci ne suka fi fuskantar hare-haren. Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar The New York Times.
Trump ya kuma yi gargadin cewa Amurka na iya sake kai hare-haren soji a Najeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci. Ya ce duk da cewa ba addini guda daya ke fuskantar matsalar ba, har yanzu a cewarsa Kiristoci su ne mafi yawan wadanda abin ya shafa.
Kalaman nasa sun haifar da martani daga Gwamnatin Tarayya, wadda ta yi watsi da ikirarin, tana mai cewa matsalar tsaro na shafar ‘yan Najeriya gaba ɗaya ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, kuma ana ci gaba da daukar matakai domin magance lamarin.
