Featured
Za Mu Sake Kai Hare-hare a Najeriya – Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai iya sake ƙaddamar da hare-hare a Najeriya idan bai gamsu da matakan da ƙasar ke ɗauka ba wajen daƙile hare-haren da ake kai wa kiristoci. Trump ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin jawabi a taron addu’ar ƙasar Amurka karo na 74 da aka gudanar a Washington.
A cewarsa, duk wanda ya kai hari kan kiristoci ya sani cewa zai fuskanci martani mai zafi daga gare shi. Trump ya ce maganar na iya zama mai nauyi, amma ya jaddada cewa gaskiya ce, yana danganta hakan da zargin kisan kiyashi da ake yi wa kiristoci a Najeriya.
A yayin taron, Trump ya yaba da halartar uwargidan Shugaban Najeriya, Remi Tinubu, inda ya bayyana ta a matsayin mace mai mutunci. Ya kuma ce hare-haren da Amurka ta kai a Najeriya a baya an yi su ne tare da haɗin gwiwar hukumomin ƙasar domin yaƙar mayaƙan IS, duk da cewa Najeriya ta ce rikicin tsaro ba ya da alaƙa da addini ko ƙabilanci.
