Featured
Gwamnatin Tinubu ta ce ta samu kuɗin shiga bayan cire tallafin man fetur amma har yanzu ta kasa magance matsalar ASUU – Atiku
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta fito ta bayyana yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur, yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ke sake barazanar tsunduma yajin aiki.
Atiku ya ce, barazanar shiga yajin aiki da ASUU ke yi ya nuna cewa, cire tallafin man bai samar da isasshen kuɗaɗen da za a inganta jami’o’in gwamnati ba. Ya ce jami’o’in na ci gaba da fuskantar ƙarancin kuɗaɗe, matsalar gine-gine, da kuma wasu batutuwan da suka shafi ma’aikata.
Read Also : Ɗan Najeriya zai iya rayuwa da Naira 3,000 a kullum – Reno Omokri
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce, gwamnati ta gabatar da cire tallafin a matsayin matakin da zai samar da kuɗaɗen inganta ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da walwalar al’umma. Ya ce dole ne a fito a yi bayanin inda kuɗaɗen suka tafi, musamman ganin yadda jami’o’i ke ci gaba da fuskantar matsaloli tare da barazanar yajin aiki.
