Connect with us

Featured

NAFDAC Ta Gargaɗi Ƴan Najeriya Kan Madarar Jabu Da Ta Ke Yawo A Kasuwa

A ranar Juma’a 22 ga Agusta, Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ta fitar da gargadi kan yaduwar madarar jabu mai suna Cowbell “Our Milk” 12g sachet a cikin Najeriya.

A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon hukumar, kamfanin Promasidor Nigeria Ltd, wanda shi ne mai lasisin kasuwanci da kuma masana’antar Cowbell “Our Milk”, ya sanar da hukumar cewa an gano wata nau’i na madara ta jabu da aka yi mata kwafin suna, kwali, lambar rijistar NAFDAC da kuma tambari.

Kamfanin ya tabbatar cewa ba shi ne ya samar da wannan madara ba, domin kwalin da aka yi amfani da shi wajen wannan jabu an daina amfani da shi tun watan Satumba, 2023.

NAFDAC ta bayyana bambanci tsakanin na gaskiya da na jabu inda ta ce: na asali na da laushi mai kama da cream, ana amfani da sabon kwali mai dauke da rubutun “Our Creamy Goodness”, ana bugun bayanan batch da injin laser, lambar sirri tana inda aka tanada a jakar, sannan yankan gefe Automatic ne. Amma na jabu ba ya kama da madara, an yi masa amfani da tsohon kwali mai rubutun “Our Milk”, an yi rubutun batch da tawada maimakon laser, an saka lambar sirri a wurin da ba daidai ba, sannan a gefe an yanke da hannu maimakon injin.

Hukumar ta kara da cewa shan wannan madara ta jabu yana iya haifar da matsalolin lafiya masu tsanani kamar cututtuka daga abinci, rashin lafiyan jiki, lalacewar gabobi, ko ma mutuwa. Ta ce jarirai, yara, mata masu juna biyu da tsofaffi ne suka fi hadari.

Saboda haka NAFDAC ta umurci daraktocin yankuna da masu kula da jihohi da su yi bincike da kuma kwashe duk wata madarar ta jabu daga kasuwa. Ta kuma ja kunnen ‘yan kasuwa da masu sayarwa da su dinga taka-tsantsan wajen saye da sayarwa.

Hukumar ta shawarci jama’a su rika sayen kayayyakin abinci daga masana’antu ko masu lasisi na hukuma, tare da bincika inganci da sahihancin kayayyakin kafin amfani. Haka kuma ta bukaci a rika kai rahoton duk wani shakku game da kayayyakin jabu zuwa ofishin NAFDAC mafi kusa ko kuma ta hanyar kiran layin kyauta 0800-162-3322 ko imel sf.alert@nafdac.gov.ng.

Haka nan, duk wani rahoto kan illa ko sakamako mara kyau daga irin wadannan kayayyaki za a iya mikawa ta shafin yanar gizon hukumar ko kuma imel pharmacovigilance@nafdac.gov.ng.

 

 

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet