Featured
NAFDAC Ta Gargaɗi Ƴan Najeriya Kan Shan Magunguna Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji amfani da magunguna ba tare da bin ƙa’ida ba, tana mai cewa hakan na barazana ga lafiya. Hukumar ta bayyana cewa amfani da magunguna fiye da kima, ƙaranci ko kuma ba bisa umarnin likita ba na iya janyo matsaloli masu tsanani wani lokacin ma har a rasa rayuka.
Daraktar Sashen Kula da Illolin Magunguna ta NAFDAC, Uchenna Elemuwa, ta ce shan magunguna kai-tsaye ba tare da shawarar ƙwararrun ma’aikatan lafiya ba, amfani da magungunan jabu da kuma yawan amfani da maganin ƙwayoyin cuta suna daga cikin manyan matsalolin da ke kawo gazawar magani da tsadar jinya.
Ta kuma yi gargaɗin cewa yawaitar amfani da maganin ƙwayoyin cuta ba tare da ƙa’ida ba na ƙara haifar da ƙwayoyin cuta masu juriyar magani. Kakaki24 ta ruwaito cewa NAFDAC ta bukaci likitoci, masu harhaɗa magunguna da jama’a su rika kai rahoton duk wata illa da suka gani daga amfani da magunguna domin kare lafiyar al’umma.
