Featured
FCCPC Ta Gudanar Da Taron Wayar Da Kai Game Da Illolin Amfani Da Sinadaran Da Ke Sa Amfanin Gona Ya Nuna Da Wuri
Hukumar Kare Haƙƙin Mai Saye da Mai Sayarwa ta Ƙasa (FCCPC) ta shirya wani taron wayar da kai a Kano domin fadakar da jama’a kan illolin amfani da sinadarai wajen hanzarta girman amfanin gona da kuma cin gurɓatattun kayayyakin abinci. An gudanar da taron ne a ranar Talata, 7 ga Oktoba, 2025, a dakin taro na Kano Foundation da ke Kofar Gadon Kaya, inda aka samu halartar masana, jami’an gwamnati, ‘yan kasuwa da kungiyoyin kare hakkin masu amfani da kayayyaki.
Mataimakin Shugaban Hukumar FCCPC, Mista Olatunji Bello, ta bakin Dakta Nkechi Mba, ya bayyana cewa manufar taron ita ce fadakar da al’umma kan hatsarin gurɓataccen abinci da muhimmancin bin ƙa’idojin gwamnati na tsaron abinci. Ya ce hukumar tana ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin da ke kula da harkokin abinci kamar NAFDAC da SON domin tabbatar da bin doka da kare lafiyar jama’a.
Masanan da aka gayyato sun yi bayani kan yadda amfani da gurɓataccen manja, man gyada, nama da sinadarai wajen sa amfanin gona ya nuna da wuri ke haifar da matsalolin lafiya kamar cutar cancer, ciwon hanta da ciwon koda. Sun bukaci jama’a da su kula da ingancin abincin da suke saya da hanyoyin sarrafa shi, domin kare kansu daga illolin da ka iya tasowa.
Hukumar FCCPC ta gargadi ‘yan kasuwa da masu sarrafa abinci da su guji amfani da dabaru ko sinadarai marasa inganci domin neman riba, tana mai jaddada cewa duk wanda aka kama yana aikata haka zai fuskanci hukunci mai tsanani. Masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yaba da wannan shiri, tare da kira da a ci gaba da irin waɗannan shirye-shiryen musamman a kasuwanni da yankunan karkara domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da ingancin abinci.
