Featured
Majalisa Za Ta Yi Doka Kan Crypto Da POS
Majalisar wakilan Najeriya ta fara ɗaukar matakai domin sanya ido kan harkokin hada-hadar kuɗaɗe ta yanar gizo, musamman waɗanda suka shafi kuɗaɗen kirifto da na’urorin POS. A ranar Litinin ne Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen, ya ƙaddamar da wani kwamiti na musamman da zai duba yadda ake amfani da waɗannan hanyoyi a fannin tattalin arziki, da kuma yadda za a samar da tsarin tsaro da kulawa na musamman.
Yayin gabatar da jawabi a wajen ƙaddamarwar, Kakakin ya bayyana cewa wannan mataki ya zama dole ne duba da yadda ake ta ƙara bayyana damuwa kan yawaitar damfara, manyan laifukan intanet, da kuma amfani da waɗannan hanyoyi wajen samar da kuɗaɗe don ayyukan ta’addanci. Ya ce rashin ingantattun dokoki da sauye-sauyen da fasahar ke kawowa sun sa dole a ɗauki matakan kare jama’a da tabbatar da gaskiya da tsari a harkokin kuɗi ta intanet.
Ya ƙara da cewa majalisar za ta tsara sabbin dokoki da zasu baiwa hukumomi damar saka idanu da tabbatar da bin ƙa’ida a mu’amalolin kirifto da POS. Haka kuma, dokokin za su kare masu amfani daga zamba, da tabbatar da cewa harkokin kuɗaɗen zamani na gudana cikin gaskiya da tsari.
Ana sa ran kwamitin zai gudanar da zaman jin bahasi da masu ruwa da tsaki daga fannoni daban-daban domin tattara bayanai da shawarwari. Wannan zai taimaka wajen tsara dokar da za ta kafa tubalin tafiyar da harkokin kuɗaɗen intanet a ƙasar cikin tsari da kariya ga ‘yan kasa.
