Connect with us

Featured

Majalisar Wakilai Ta Fara Bincike Kan Aikin CCTV Na Dala Miliyan 460 a Abuja

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da gudanar da bincike kan aikin CCTV mai darajar dala miliyan 460 da aka kaddamar a Abuja, bayan ƙaruwar matsalar tsaro da asarar rayuka a Babban Birnin Tarayya. Wannan mataki ya biyo bayan kudurin gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar Isuikwuato/Umunneochi daga Jihar Abia, Amobi Godwin Ogah, ya gabatar a zaman majalisa. Ogah ya bayyana takaici cewa duk da wannan babban jari da aka zuba a tsarin, har yanzu laifuka da satar mutane ƙaruwa su ke a Abuja.

Ogah ya tuna cewa tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ce ta fara aikin CCTV domin inganta tsaro da sa ido a manyan wurare a Abuja. A cewarsa, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniya da kamfanin ZTE Communications na kasar Sin a shekarar 2010, ta hannun tsohon Ministan Kudi Dr. Olusegun Aganga, inda aka amince da rance daga China EXIM Bank na dala miliyan 460 daga cikin tallafin bashi na dala miliyan 600, da wa’adin biyan bashin shekaru 20 gaba ɗaya.

Sai dai ya bayyana damuwa cewa duk da cewa Najeriya tana ci gaba da biyan bashin, tsarin CCTV ɗin bai taɓa aiki yadda ya kamata ba, kuma matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara. Ya ce wannan yanayi ya sa ƙasar ta shiga asara a kowane ɓangare, domin ana biyan bashin aikin da bai haifar da wata fa’ida ba ga tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Bayan tattaunawa daga wasu ’yan majalisa ciki har da Billy Osawaru daga Jihar Edo, majalisar ta yanke shawarar kafa kwamitin wucin gadi domin bincikar yadda aka kashe kuɗin rancen da kuma gano dalilin da yasa aikin bai yi tasiri ba. Kwamitin zai gayyaci duk hukumomin gwamnati da kamfanonin da suka taka rawa a aikin, sannan ya gabatar da rahoto ga majalisar don daukar matakin doka.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet