Connect with us

Featured

Harsashi Ya Yi Ajalin Direban Adaidaita-sahu a Lagos

Wani matuƙin Adai-daita-sahu (keke Napep) ya rasa ransa sakamakon wani harsashi da ya sameshi a wajen otal ɗin (brothel) da ke unguwar Badore, Ajah, a jihar Lagos. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, 2025, lokacin da mamacin ya fita daga cikin otal ɗin don sayen ruwa a shagon da ke kusa. Sai wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka bayyana a cikin mota suka fara harbi babu kakkautawa, inda ɗaya daga cikin harsasan ya same shi.

 

Wani jami’in ‘yan sanda da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, “mutumin ya gama aiki da yamma, ya tafi wurin hutawa ne. Da ya fita don sayen ruwa, sai wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne suka fara harbi, harsashi ya same shi ya mutu nan take.” Shaidun gani da ido sun ce maharan sun zo ne da mota kirar Toyota Corolla mai launin shuɗi, inda suka rika harbi ba tare da nufi kai tsaye ga wanda aka kashe ba.

 

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa harbin yana da alaƙa da rikicin kungiyoyin asiri da ake fafatawa a yankin. Sun ce wani aka yi niyyar harba, amma sakamakon harbin bazata ne ya rutsa da marigayin wanda bai san da komai ba. Wannan lamari ya ƙara jefa al’umma cikin tsoro da damuwa game da yawaitar irin wannan tashin hankali.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Lagos, Abimbola Adebisi, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an samu gawar mamacin a safiyar washegari, kuma aka kai ta dakin ajiye gawa, kafin daga bisani a mika ta ga iyalansa domin binne shi. Wannan na zuwa ne bayan wasu hare-haren kungiyoyin asiri a wasu sassan jihar da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a watannin baya-bayan nan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet