Featured
Tinubu ya Karrama Tawagar Ƙwallon Kwando Ta Mata Da Dala $100,000, Duk Mutum Ɗaya
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama tawagar kwallon kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, da kyaututtuka masu tarin yawa, ciki har da $100,000 ga kowacce ’yar wasa, da kuma $50,000 ga kowane memba daga cikin kwamitin koyarwa da fasaha guda 11.
Tinubu ya kuma bai wa duka ’yan tawagar da ma’aikatansu gida mai dakuna uku a sabon Renewed Hope Estate.
Baya ga haka, Shugaban kasar ya ba su lambar yabo ta kasa mai daraja — Officer of the Order of the Niger (OON).
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya sanar da hakan yayin taron karramawa da aka shirya a dakin liyafa na fadar shugaban kasa, Abuja.
Tawagar D’Tigress tare da jami’anta sun samu kyakkyawar tarba daga uwargidar shugaban kasa, Senator Oluremi Tinubu, tare da uwargidar mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Shettima, da misalin karfe 5:05 na yamma a New Banquet Hall na Fadar Shugaban Kasa.
A madadin Shugaba Tinubu, Shettima ne ya karɓi tawagar domin nuna godiya da yabo bisa nasarar da suka samu.
Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci taron sun hada da:
Femi Gbajabiamila, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa
Garba Maidoki, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Matasa da Wasanni
Kabiru Amadou, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Wasanni
D’Tigress sun samu wannan tarba ta musamman ne bayan da suka lashe kofin AfroBasket na mata karo na biyar a jere, inda suka lallasa Mali da ci 78–64 a wasan karshe da aka buga a Palais des Sports de Treichville, Abidjan, Côte d’Ivoire.
Wannan bikin karramawa ya biyo bayan irin taron da Shugaba Tinubu ya shirya makon da ya gabata domin karrama kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasa, Super Falcons, bayan sun lashe kofin WAFCON karo na goma a Rabat, Morocco.
