Connect with us

Featured

Ƴar Asalin Jihar Yobe Ta Zama Zakara A Gasar Harshen Turanci Ta Duniya

Nafisa Abdullah Aminu, daliba ‘yar shekara 17 daga Jihar Yobe, ta samu lambar yabo a matsayin “Mafi Cancanta a Fasahar Harshen Turanci ta Duniya” a gasar TeenEagle Global Finals da aka gudanar a birnin London, ƙasar Birtaniya a shekarar 2025.

Nafisa ta wakilci Najeriya ta hanyar makarantar Nigerian Tulip International College (NTIC), inda ta kayar da sama da ɗalibai 20,000 daga ƙasashe 69, abin da ya zama wani tarihi, kuma ya ɗaga sunan jihar Yobe da Najeriya a idon duniya.

Gasar TeenEagle wata gasa ce da ake ɗauka a matsayin mai matuƙar muhimmanci a fagen koyon Turanci, tunani mai zurfi da kuma kwarewar sadarwa — ga ɗalibai daga ƙasashen da ke da Turanci a matsayin harshen uwa da waɗanda ba haka ba.

Wannan nasara ta Nafisa ta samu tabbaci ne daga wani makusancinta, Hassan Salifu, wanda ya danganta nasararta ga himma, ladabi da kuma goyon bayan da gwamnatin jihar Yobe ta bai wa fannin ilimi.

“Nasarar ’yarmu a matakin duniya ba za ta yiwu ba da ba tare da hangen nesa da goyon bayan Gwamna Mai Mala Buni ba, wanda ya bai wa ilimi muhimmanci har ta kai ga kawo girma da kima ga jiharmu da ƙasarmu gaba ɗaya,” in ji Salifu kamar yadda jaridar Leadership ta rawaito.

Ya ƙara da cewa Nafisa ta zarce ‘ya’ya daga ƙasashen da ke amfani da Turanci a matsayin harshen uwa, wanda hakan ke nuna matakin ƙwazonta da shirin da ta yi sosai.

Wannan nasara ta haifar da murna a cikin jihar Yobe da ma Najeriya gaba ɗaya, inda iyalanta suka nuna godiya ga Gwamna Buni da malamai a NTIC saboda rawar da suka taka wajen gina hazakanta.

“Nasarar Nafisa hujja ce ta yadda saka hannun jari a fannin ilimi ke iya canza rayuwa. Kokarin Gwamna Buni ya jawo ci gaban makarantu tare da fidda jihar Yobe da Najeriya gaba ɗaya zuwa gaban duniya,” in ji iyalanta.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet