Featured
Har Yanzu Ba’a Bamu Dala $100, 000 Da Gwamnati Ta Yi Mana Alƙawari Ba – Super Falcons
Kyaftin ɗin Super Falcons kuma yar wasan gaba, Rasheedat Ajibade, ta bayyana takaicinta game da jinkirin biyan alawus da kuɗaɗen da aka yi wa tawagarsu alkawari.
Ta bayyana haka ne a wata hira da aka yi da ita a sabon shirin “With Chude” da fitaccen mai gabatarwa Chude Jideonwo ke shiryawa.
Ajibade ta ce har yanzu ‘yan wasan ba su samu kuɗin da aka yi musu alkawari na dala dubu 100 da sauran hakkokinsu ba, duk da alkawuran da hukumomi ke maimaitawa.
“Ba mu samu kuɗinmu ba, Duk alkawuran da kuka ji ana ta yaɗawa, har yanzu ba mu samu kome ba,” in ji ta.
Ajibade ta ƙara da cewa an shaida musu cewa an ware kuɗin, amma har yanzu ba su same su ba.
“Mutane suna roƙo. Har yanzu ba mu samu ba. Idan sun biya za ku gani. Har ma da kuɗin ladan wasanninmu da komai… “.
‘Yar shekara 24 dai ta roƙi hukumomi su cika alkawuran da suka yi, tana mai cewa jinkirin yana shafar rayuwar ‘yan wasan.
Bayan nasarar tarihi da Super Falcons suka samu na lashe kofin Women’s Africa Cup of Nations karo na 10 a Morocco, Shugaba Bola Tinubu a watan Yuli 2025 ya sanar da kyautar kuɗi na dala dubu 100 ga kowace ‘yar wasa, tare da sauran tagomashi.
