Featured
Rundunar Ƴan sandan Jihar Kano Ta Sha Alwashin Tabbatar Da Ingantaccen Tsaro a Zaɓen Cike-Gurbi
Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta tabbatar wa mazauna jihar cewa za ta samar da tsaro mai inganci yayin gudanar da zaben cike-gurbi a mazabar Bagwai/Shanono da Ghari/Tsanyawa a ranar Asabar 16 ga Agusta 2025.
Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar, Ibrahim Bakori, ne ya bayyana hakan ta wayar tarho yayin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Juma’a 15 ga Agusta a Kano.
Bakori ya ce hukumomin tsaro a jihar na aiki tare domin tabbatar da gudanar da zaben cike-gurbi cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.
Ya bayyana cewa an bayar da umarni ga jami’an da aka tura domin samar da tsaro a kowanne rumfar kada kuri’a a yankunan kananan hukumomin da abin ya shafa.
Ya kara da cewa an tanadi tsare-tsaren tsaro na musamman da za su tabbatar da yanayin siyasa mai cike da lumana a jihar.
Kwamishinan ya tabbatar wa dukkan ‘yan kasa masu bin doka cewa za su iya fita kada kuri’a a ranar Asabar ba tare da tsoro ba.
Ya shawarci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su gudanar da harkokinsu cikin lumana da kuma bin doka wajen gudanar da zaben.
Ya ce, “Za mu kasance a fili a rumfunan kada kuri’a domin kare hakkokin masu kada kuri’a da hana tsoratarwa.
“Ba za mu lamunci ta’addanci, tsoratarwa da duk wani nau’in tashin hankali kafin, yayin, da bayan zabe ba.
“Za mu samar da daidaitacciyar dama ga dukkan jam’iyyun siyasa, kuma duk wani aiki da zai iya haifar da rudani a jihar ba za mu lamunta ba.”
Bakori ya gargadi cewa duk wanda aka kama yana karya doka za a kama shi a gurfanar da shi a kotu.
NAN
