Featured
Har Yanzu Ba Mu Karɓi Umarnin Kotu kan Dakatar Da Dokar Lasisin Gilashin Mota Mai Duhu Ba – Rundunar Ƴan Sanda
Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya ta bayyana cewa har yanzu ba ta karɓi umarnin kotu ba wanda ya dakatar da aiwatar da shirin bayar da lasisin gilashin mota mai duhu (tinted glass permit). Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a ranar Asabar, yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa kotu ta hana ‘yan sanda kama ko gurfanar da masu motoci da ke amfani da gilashin mota mai duhu.
Kotun Tarayya da ke Warri, Jihar Delta, ce ta bayar da wannan umarni a ranar Juma’a a cikin shari’ar da lauya John Aikpokpo-Martins ya shigar, mai lamba FHC/WR/CS/103/2025, inda ake karar Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa da Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya. Kotun ta umurci ‘yan sanda da su dakatar da aiwatar da tsarin lasisin gilashin mota mai duhu har sai an gama sauraron shari’ar gaba ɗaya.
Sai dai CSP Hundeyin ya bayyana a shafinsa na X cewa rundunar ba ta samu takardar hukuncin kotu ba tukuna. Ya kuma zargi wasu da yin rarraba sassan hukuncin ta yadda zai nuna gefe ɗaya kawai, maimakon cikakken bayani. Ya bayyana cewa “duk da cewa ba mu samu kwafin hukuncin ba tukuna, bari in nuna muku sakin layi na takwas domin cikakken hoto, ba wai na shida kawai da kuka yada ba.”
Tun a watan Afrilu na shekarar 2023 ne rundunar ‘yan sanda ta sanar da komawa tsarin bayar da lasisin gilashin mota mai duhu ta hanyar tsarin POSSAP bayan ta dakatar da shi a 2022. Wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce daga kungiyoyin lauyoyi da ‘yan kasa, wadanda ke ganin tsarin ya saba wa kundin tsarin mulki.
