Featured
Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane 180 Daga Hannun Ƴan Ta’adda
Hedikwatar Tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun samu gagarumar nasara a yaki da ta’addanci da laifuka a sassa daban-daban na ƙasar a watan Satumba. A cewar Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Manjo Janar Markus Kangye, sojoji sun cafke mutane 450 da ake zargi da ta’addanci da fashi, yayin da wasu 39 daga cikinsu suka mika wuya. Haka kuma, an ceto fararen hula 180 daga hannun ‘yan ta’adda a yayin hare-hare daban-daban da rundunar ta kai.
A cikin bayaninsa, Kangye ya ce sojojin sun kwace makamai 63 da harsasai 4,475 da kuma kayan yaƙi daban-daban guda 294, ciki har da grenades, na’urorin sadarwa, babura da motocin da ake amfani da su wajen aikata laifuka. Rundunar ta Operation DELTA SAFE kuma ta dakile satar man fetur da darajarsa ta kai sama da Naira miliyan 112, inda ta lalata matatun tace man fetur na haram 41 tare da kwace dubban lita na danyen mai da sauran kayayyaki.
A yankin Arewa maso Gabas, rundunar Operation HADIN KAI tare da haɗin gwiwar rundunar sama, dakarun haɗaka da ƙungiyoyin tsaro na gari sun gudanar da jerin hare-hare tsakanin 23 zuwa 30 ga Satumba. An kai farmaki a yankuna kamar Konduga, Gwoza, Monguno da Damboa a Jihar Borno; Madagali da Mubi a Adamawa; da Gujba a Yobe. Wannan ya haifar da halaka ‘yan ta’adda da dama, rushe sansaninsu da katse hanyoyin samar musu da kayan aiki.
Hedikwatar Tsaron ta ce za ta ci gaba da bayar da rahotannin wata-wata don nuna cigaba da jajircewar rundunonin tsaro wajen yakar ta’addanci, hana fashi da makami da tabbatar da zaman lafiya a dukkan sassan ƙasa. Wannan mataki na dakarun ya kuma bai wa al’ummomi damar komawa gidajensu da cigaba da ayyukan gona ba tare da tsoron farmakin ‘yan ta’adda ba.
