Featured
Babban Hafsan Sojin Ƙasa Ya Sha Alwashin Inganta Rayuwar Sojoji
Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa za a kawo ƙarshen ƙalubalen da sojoji ke fuskanta kai tsaye domin magance su yadda ya kamata.
Ya ce tare da goyon bayan Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shugabancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ana ɗaukar matakai na musamman don inganta rayuwar sojoji da iyalansu.
Oluyede ya faɗi haka ne a ranar Laraba 20 ga Agusta yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a ƙarshen ziyarar kwanaki uku da ya kai Hedikwatar Rundunar Sojojin Najeriya ta Rukuni na 6 da ke Fatakwal.
A yayin ziyarar, shugaban sojojin ya kaddamar da wasu ayyuka, ya yi jawabi ga dakarun rundunar, tare da ganawa da manyan masu ruwa da tsaki a yankin Neja-Delta.
Oluyede ya jaddada cewa walwalar sojoji na da matuƙar muhimmanci a wurinsa saboda yana da alaƙa da kwarin gwiwar da sojoji ke buƙata wajen aiwatar da ayyukansu. Ya ce wannan ziyara ta bashi damar fahimtar matsalolin dakarun da idonsa.
