Connect with us

Featured

Gwamnan Gombe Ya Soki Gwamnatin Tarayya Kan Biyan Naira Biliyan 1.4 Ga Sansanin Tubabbun Boko Haram

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan adadin kuɗin da gwamnatin tarayya ta biya a matsayin diyya saboda kwace sansanin NYSC na jihar domin gudanar da shirin Operation Safe Corridor.

Shirin OPSC da ke Kwami, Malam Sidi, na ƙarƙashin jagorancin rundunar tsaro ta ƙasa ne domin yi wa masu tuba daga Boko Haram horo da gyaran hali tare da dawo da su cikin al’umma.

Wannan sansani an gina shi ne a zamanin mulkin tsohon gwamna Ibrahim Dankwambo domin gudanar da mako uku na horarwar ga matasan da aka tura hidimar ƙasa (NYSC) a jihar.

Da yake magana ta bakin sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Njodi, yayin da ya karɓi tawagar manyan jami’an rundunar tsaro daga hedikwatar tsaro a ranar Talata, Gwamna Yahaya ya bayyana cewa an tilasta wa jiharsa ta fara gina sabon sansanin NYSC a yankin Boltongo bayan an kwace na Malam Sidi.

Yahaya ya ce: “Gwamnatin tarayya ta biya mu diyya Naira biliyan 1.4 kacal, alhali mu mun riga mun kashe fiye da Naira biliyan 5 wajen gina sabon sansanin NYSC. Wannan kuwa kusan ninki uku na kuɗin da aka ba mu ne.”

Ya bayyana cewa duk da shakku na farko da jama’ar yankin suka nuna, haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da hukumomin tsaro ya taimaka wajen samun amincewar al’umma.

“Ta hanyar tattaunawa akai-akai da kuma tsara dabaru na musamman, mun samu nasarar kawar da fargabar jama’armu, musamman a Malam Sidi inda ake gudanar da shirin,” in ji shi.

Yahaya ya sake jaddada goyon bayan gwamnatinsa ga nasarar shirin Operation Safe Corridor, tare da tabbatar wa dakarun ƙasa cewa Jihar Gombe za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro wajen gyara da dawo da masu tuba cikin al’umma.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet