Connect with us

Featured

Ƙarin Kuɗin Fasfo A Najeriya Take Haƙƙin Dan Adam Ne – SERAP

Kungiyar kare haƙƙin jama’a ta SERAP, ta roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta janye sabon ƙarin kuɗin fasfo da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta sanar. Kungiyar ta ce ƙarin da aka yi ba bisa ƙa’ida ba ne, zalunci ne kuma ya ƙeta haƙƙin bil’adama na ‘yan ƙasa.

Hukumar Shige da Fice ta sanar cewa daga ranar 1 ga Satumba, 2025, kuɗin fasfo shafi 32 mai shekara biyar zai koma ₦100,000, yayin da na shafi 64 mai shekara goma zai koma ₦200,000. Wannan na zuwa ne shekara guda kacal bayan irin wannan ƙarin da aka yi a Satumba 2024, abin da ya haifar da cece-kuce a tsakaninyan ƙasa.

A wata wasiƙa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya sanya wa hannu a ranar 30 ga Agusta, 2025, ta ce wannan ƙarin zai hana miliyoyin talakawa samun fasfo, ya kuma tauye haƙƙin ɗan ƙasa da doka ta tabbatar. Kungiyar ta ce ƙarin kuɗin ya saba wa tanade-tanaden Sashe na 2 da na 4 na Kundin Tsarin Mulkin 1999.

Kungiyar ta yi gargadin cewa sabon kuɗin zai ƙara jefa ‘yan ƙasa cikin wahala, musamman masu ƙaramin karfi. SERAP ta ce Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, da Shugabar Hukumar Shige da Fice, Kemi Nandap, ba su yi la’akari da halin kuncin da al’umma ke ciki ba kafin amincewa da wannan karin. Ta kuma yi barazanar gurfanar da gwamnati a kotu idan ba a janye shi cikin kwanaki bakwai ba.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet