Connect with us

Featured

Uba Sani Ba Abokina Ba Ne Yarona Ne A Siyasa – El-Rufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba shi da wata alaƙa ta musamman da gwamnan mai ci, Uba Sani, inda ya ce dama ba abokinsa ba ne, illa dai yaronsa ne da ya ɗaura a hanya. Ya ce a tsarinsa duk inda ya bari to ba ya komawa, sai dai idan an nemi shawararsa, kuma a halin yanzu ma ba sa magana da Gwamna Uba Sani.

El-Rufai ya bayyana haka ne a hirarsa da tashar Channels, inda ya jaddada cewa rashin abota tsakaninsa da gwamnan ba ya nufin rikici su ke, sai dai kawai al’ada ce ta siyasa. A cewarsa, “yarona ne a siyasa, wanda na ɗaura a hanya, amma yanzu ba ma magana.” Ya ce duk da haka yana alfahari da ganin mutane da ya taimaka sun samu daukaka a siyasa da sauran fannoni.

A game da tikitin Musulmi-Musulmi na shekarar 2023, El-Rufai ya kare goyon bayansa, inda ya ce lissafin siyasa ne kawai domin nasara, ba wai batun addini ba. Ya ƙara da cewa babu wani Kirista a Kaduna da aka tauye wa haƙƙinsa a lokacin da ya yi amfani da tsarin Musulmi-Musulmi a gwamnatinsa.

Sai dai ya yi nuni da cewa taimakonsa wajen kawo mutum kan mulki ba zai hana shi yin suka idan an kauce hanya ba. A cewarsa, rashin yin magana kan kura-kurai saboda an taɓa taimaka wa mutum shi ne ya sa ƙasar ta shiga mawuyacin hali a yanzu.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet