Featured
Rundunar Ƴan Sandan Kano Ta Kama Mutane 107 Sakamakon Aikata Laifuka Mabanbanta
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke mutane 107 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a watan Agusta, 2025. Wannan na cikin matakan da aka ɗauka karkashin shirin “Operation Kukan Kura”, wanda aka kaddamar a ranar 1 ga watan Yuli, 2025, domin magance matsalolin tsaro a jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ne ya bayyana hakan a yau Litinin 01 ga Satumba, 2025, a taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai. Ya ce cikin wadanda aka cafke akwai masu fashi da makami 8, masu garkuwa da mutane 8, masu fataucin mutane 3, masu safarar miyagun ƙwayoyi 14, barayin motoci 2, barayin babura 6, sauran barayi 5 da kuma ‘yan daba 61. Rundunar kuma ta kubutar da mutum guda da aka yi garkuwa da shi.
A cewar Bakori, rundunar ta kuma kwato makamai da kayan da aka yi amfani da su wajen aikata laifuka, ciki har da bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, bindigogi kirar gida bakwai, harsasai 11, motoci 8, babura 8, shanu 8, adda 102, wukake 74 da kuma wayoyi 59. Haka kuma an gano tabar wiwi mai nauyi, magungunan ƙwayoyi daban-daban, robobin sholisho 211, kwalaben sukurdaye 257, katunan cire kuɗi na Opay 17 da kuma POS guda 3.
Kwamishinan ya yaba wa al’ummar Kano bisa haɗin kai da goyon bayan da suke baiwa ‘yan sanda, musamman wajen samar da bayanai. Ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bada rahoto kan duk wani abin da ya yi kama da laifi, tare da tabbatar musu cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
