Featured
Britaniya Za Ta Haramta Sayar da Lemukan Ƙara Kuzari Ga Ƙananan Yara
Gwamnatin Birtaniya ta sanar da shirin dakatar da sayar da lemuka masu ƙara kuzari na “energy drinks” masu ɗauke da sinadarin caffeine mai yawa, kamar Red Bull, ga yara ƴan ƙasa da shekara 16 a Ingila. Ministan Lafiya, Wes Streeting, ya bayyana matakin a ranar Laraba 03 ga Satumba, yana mai cewa manufar ita ce kare lafiya da walwalar matasa.
Kididdigar gwamnati ta nuna cewa kusan ɗaya cikin uku na matasan da shekarunsu ke tsakanin 13 zuwa 16 suna yawan shan waɗannan lemuka, waɗanda galibi ke ƙunshe da caffeine. Wannan na daga cikin abubuwan da ke haifar da damuwa ga iyaye da malamai.
Yawancin manyan shagunan sayar da kaya tuni suka fara bin ƙa’idar hana yara waɗannan lemuka, amma wannan sabon tsarin zai maida shi doka ta ƙasa baki ɗaya. Hakan zai tabbatar da cewa babu yaro da zai iya samun damar saya a ko’ina cikin ƙasar.
