Connect with us

Featured

NECO Ta Rage Adadin Yawan Tambayoyin Jarabawar Turanci Daga 100 Zuwa 80

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta sanar da rage yawan tambayoyin zaɓi na Paper III a darasin Turanci daga 100 zuwa 80, wanda hakan zai fara aiki ne daga jarabawar SSCE na cikin gida ta shekarar 2026. Sanarwar, wacce ta fito daga Ofishin Kwamishinan NECO na Jihar Osun, Sunday K. Bolaji, mai ɗauke da kwanan wata 1 ga Satumba, 2025, ta bayyana cewa sabon tsarin ya ƙunshi sassa guda shida.

Sabbin sassan sun haɗa da: Antonyms (tambayoyi 10), Registers (10), Idioms, Phrasal Verbs da Foreign Words (10), Synonyms (10), Grammatical Structures (30), sannan Cloze Test (10). Lokacin da za a ware don wannan Paper III kuwa an rage shi zuwa mintuna 50. Wannan gyara, a cewar hukumar, zai sauƙaƙa tsarin jarabawa tare da inganta yadda ɗalibai ke fuskantar jarrabawar.

A baya an ruwaito cewa, a ranar 29 ga Agusta 2025, NECO ta tabbatar da cewa daga watan Nuwamba/Disamba 2025 za ta fara amfani da tsarin Computer-Based Test (CBT) wajen gudanar da SSCE na waje, maimakon tsohuwar hanyar takarda da biro. Wannan mataki ya yi daidai da umarnin Gwamnatin Tarayya na watan Yuli 2025, wanda ya buƙaci a yi amfani da cibiyoyin CBT na gwamnati da na masu zaman kansu wajen gudanar da jarabawar SSCE daga shekarar 2026.

Hukumar ta kuma gayyaci masu cibiyoyin CBT a fadin ƙasar nan da su nemi samun takardar izini, bisa sharudda na musamman na fasaha, kayan aiki, da tsaro, domin tabbatar da ingancin jarabawa da nasarar aiwatar da tsarin. Wannan sabon salo na NECO zai taimaka wajen zamanantarwa tare da inganta tsarin jarabawa a Najeriya, rage maguɗin jarabawa, da faɗaɗa damar karatu ta hanyar amfani da fasahar zamani.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet