Featured
Shugaba Tinubu Zai Tafi Faransa Domin Hutun Shekara
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tashi daga Abuja yau Alhamis, 4 ga Satumba, domin fara hutun shekara ta 2025. Rahoton da fadar shugaban kasa ta fitar ya bayyana cewa Tinubu zai dauki tsahon kwanaki goma domin hutawa.
A lokacin wannan hutu, shugaban kasa zai shafe lokacinsa a ƙasashen Faransa da Birtaniya.
Wannan hutu ya yi daidai da kundin tsarin mulki, wanda ya bawa shugaban damar yin hutu a cikin shekara, kazalika hutun yana bashi damar gudanar da wasu muhimman ziyarce-ziyarcen aiki a ƙasashen waje.
Ana sa ran shugaban kasa zai dawo ƙasar bayan kammala hutun. Kamar yadda mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya sanar a ranar Alhamis 04 ga Satumba, 2025.
