Featured
An Gano Wani Gurneti a Cikin Jikin Wani Matashi a Faransa
Wani asibiti a birnin Toulouse da ke kudancin Faransa ya gano wani gurneti na Yaƙin Duniya na Ɗaya a cikin duburar wani matashi ɗan shekara 24. Lamarin ya faru ne da daren 31 ga Janairu, lokacin da matashin ya je sashen gaggawa na Asibitin Rangueil yana kuka da matsanancin ciwo.
Rahotanni sun ce matashin ya shaida wa likitoci cewa ya saka wani abu a jikinsa, amma bai bayyana menene ba. Sai dai yayin aikin cire abin, likita ya gano cewa gurneti ne mai tsawon kusan santimita 16, lamarin da ya tilasta kiran jami’an tsaro da tawagar kwance bama-bamai.
Bayan bincike, kwararrun masu kwance bama-bamai sun tabbatar da cewa gurnetin tsoho ne kuma bashida wani hadari, don haka bai zama barazana ba. Har yanzu ana kula da lafiyar matashin a asibiti, yayin da ofishin mai gabatar da ƙara na Toulouse ya buɗe bincike domin gano yadda abin ya shiga jikinsa.
