Featured
An Sace Sojoji 45 A Colombia
Rundunar sojin Colombia ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da akalla sojoji 45 a yankin Cauca, wani yanki da ke ƙarƙashin tasirin wani bangare na tsohuwar kungiyar ’yan tawaye ta FARC.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace sojojin ne yayin da suke gudanar da wani aiki a yankin. Ministan tsaron ƙasar, Pedro Sanchez, ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa daruruwan mutane ake zargi da hannu a harin.
Ya kuma gargadi masu hannu da cewa hukumomi za su tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Yankin Cauca dai na daga cikin wuraren da ake noma Coca, wanda ake sarrafawa a matsayin kayan hada hodar ibilis.
