Connect with us

Featured

Matatar Mai ta Dangote Ta Karyata Jita-jitar Cewa Za Ta Rufe Sashen Fetur Na Tsahon Watanni Biyu

Matatar Mai ta Dangote ta musanta rahotonnin da ake yaɗawa cewa za ta rufe sashen samar da fetur na tsawon watanni biyu zuwa uku. Mai magana da yawun kamfanin, Anthony Chiejina, ya bayyana labarin a matsayin ƙarya. Rahoton Reuters ya ce ana iya dakatar da sashen saboda matsalar “catalyst leaks”, amma Chiejina ya ce babu gaskiya a zancen.

Masana sun bayyana cewa tun daga watan Janairu 2024, Matatar Mai ta Dangote ta rage dogaro da Najeriya kan shigo da fetur daga Turai da Birtaniya daga ganga 200,000 a rana zuwa kusan ganga 120,000 a cikin rabin farkon shekarar 2025. Haka kuma, kamfanin ya aika da jiragen mai zuwa Amurka, wanda masana suka bayyana hakan a matsayin babban cigaba.

Matatar Mai ta Dangote na shirin ƙara ƙarfin aiki zuwa ganga 700,000 a rana nan da watan Disamba 2025. A watan Agusta kuwa, kamfanin ya fara shigo da man Sankofa daga Ghana, wanda ya fi nauyi fiye da nau’in mai da aka saba sarrafawa a nan. Wannan ya nuna yadda masana’antar ke iya daidaitawa wajen amfani da nau’ikan mai daban-daban daga ƙasashe.

Rahoton ya kuma bayyana cewa Matatar Mai ta Dangote ta shigo da mai a watan Yuli 2025 da kusan ganga 570,000 a rana. Yawancin wannan daga Amurka ya fito, wanda ya zarce na Najeriya saboda ƙalubalen samar da isasshen man gida da kuma arha. Yanzu masana sun kiyasta aikin matatar yana gudana da kusan ganga 445,000 a rana, wato 68%, tare da shirin gyara da zai iya ragewa zuwa ganga 400,000 a lokacin Disamba zuwa JaDangotenairu.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet