Featured
Mamakon Ruwan Sama Ya Janyo Jinkirin Tashin Jiragen Air Peace a Lagos
Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya sanar da jinkirin tashi da saukar wasu jiragensa a fadin Najeriya sakamakon ruwan sama mai tsanani da aka samu a Lagos tun safe a ranar Talata 16 ga Satumba, 2025.
Kakakin kamfanin, Osifo-Whiskey Efe, ya bayyana cewa matsanancin yanayin ya shafi jadawalin tashi da saukar jiragen, amma sun tabbatar da cewa lafiyar fasinjoji ita ce mafi muhimmanci a gare su.
Air Peace ta ce tana kokarin rage tasirin wannan jinkiri, tare da neman hakurin fasinjoji, inda ta shawarci masu son karin bayani su tuntube ta ta waya ko imel domin samun sabbin jadawalin tashi.
Hukumar (NiMet) ta riga ta yi hasashen ruwan sama mai dauke da hadari daga Litinin zuwa Laraba a wasu sassan kasar, ciki har da jihohin Arewa da kuma tsakiyar Najeriya, inda aka yi gargadin yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu yankuna.
