Featured
Saudi Arabia Ta Saki ƴan Najeriya Uku da Aka Tsare Bisa Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
Hukumomin Saudi Arabia sun saki wasu ƴan Najeriya uku da aka tsare a birnin Jidda bayan an zarge su da safarar miyagun ƙwayoyi. Mutanen sun haɗa da Maryam Hussain Abdullahi, Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddieq. Mutanen dai sun yi balaguro zuwa ƙasar Saudiyya ne domin yin Umrah, inda aka kama su bayan saukarsu daga jirgi.
Rahotanni sun nuna cewa, wasu gungun mutane da ke aiki a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Mallam Aminu Kano (MAKIA) ake zargi da manna sunayen mutanen uku a wasu akwatunan da ke ɗauke da miyagun ƙwayoyi. Hukumar yaki da safarar miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ce ta sanar da sakin mutanen uku, inda ta bayyana cewa sun shiga jirgin Ethiopian Airline ET940 daga Kano zuwa Jidda a ranar 6 ga watan Agusta, 2025.
Bincike ya gano cewa wani mai shekara 55 mai suna Mohammed Ali Abubakar, wanda aka fi sani da Bello Karama, shi ne jagoran ƙungiyar da ake zargi da musanya akwatunan. Rahoton NDLEA ya ce Bello Karama ya yi hadin gwiwa da wasu mutane ciki har da ma’aikacin jirgin don aikata wannan aika-aikar.
Tuni aka gabatar da tuhume-tuhume a kan waɗanda ake zargi da hannu a safarar miyagun ƙwayoyin, ciki har da Mohammed Ali Abubakar, Celestina Emmanuel Yayock, Abdulbasit Adamu Sagagi da Jazuli Kabir. Hukumomi sun ce bincike zai ci gaba domin tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da laifi.
