Connect with us

Featured

Ƴan Damfara Na Ɓata Sunan Najeriya A Ƙasashen Waje – EFCC

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gargadi matasa kan yadda karuwar zamba ta intanet ke ɓata sunan Najeriya a idon duniya tare da tsananta shingen visa ga ‘yan kasa masu bin doka. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana haka a wani taro da Kungiyar Matasa kan Tsaro ta shirya a Fatakwal, yana mai cewa laifukan zamba, almundahanar kudi da cin amana suna jawo wa kasa asarar biliyoyin naira da kuma hana ci gaban tattalin arziki.

Olukoyede ya bayyana cewa irin wadannan laifuka ba kawai suna lalata makomar masu aikata su ba ne, har ma suna bata sunan Najeriya, wanda hakan ke jawo wa ‘yan kasa masu gaskiya matsaloli wajen samun izinin tafiya kasashen waje. Ya shawarci matasa su karkata karfinsu zuwa sahihin aiki kamar kirkire-kirkiren dijital, noma, kasuwanci da harkokin fasaha maimakon fadawa tarkon zamba.

Shugaban EFCC ya kara da cewa “zamba ba nasara ba ce, tarko ce.” Ya kuma jaddada kudirin hukumar na ci gaba da wayar da kai, gudanar da bincike da kuma karfafa hadin gwiwa da al’umma domin dakile laifukan tattalin arziki.

A yayin taron, Hukumar NDLEA ta gargadi matasa kan illar shan miyagun kwayoyi, yayin da NSCDC ta yi kira da a guji lalata bututun mai a yankin Kudu maso Kudu. EFCC ta kuma jaddada cewa ta karfafa fatattakar ‘yan damfara a fadin kasar, inda ta kama masu aikata laifukan yanar gizo da kuma samun hukuncin kotu kan wasu daga cikinsu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet