Connect with us

Featured

Amincewa da Kasar Falasɗinu Taimakon Ta’addanci Ne – Netanyahu

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya zargi shugabannin kasashen Yamma da suka amince da kafa kasar Falasɗinu da mara wa ta’addanci baya. Ya ce Falasɗinawa ba za su taba samun kasarsu ba, tare da bayyana cewa Isra’ila za ta dauki mataki kan sanarwar da kasashen Birtaniya, Canada, Australia da Portugal suka yi na amincewa da kafa kasar Falasɗinu.

 

Rahotanni sun ce a yau Litinin 22 ga Satumba, ana sa ran Faransa da wasu kasashen Turai za su sanar da irin wannan mataki a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake gudanarwa a birnin New York. Wannan ya nuna yadda matsin lambar kasa da kasa ke kara karfi kan batun Falasɗinu da Isra’ila.

 

Shugaban Falasɗinawa, Mahmud Abbas, ya ce amincewa da Falasɗinu a matsayin kasa mataki ne na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya. Sai dai Amurka ta kira matakin kasashen Yamma a matsayin yunkurin neman suna, tana mai jan hankalin kasashen duniya kan abin da ta kira rashin daidaito.

 

A bangare guda kuma, rahotanni daga Gaza sun bayyana cewa an kashe karin Falasɗinawa 71 a ranar Lahadi 21 ga Satumba, sakamakon hare-haren Isra’ila, lamarin da ya kara tayar da hankula kan rikicin da ke kara tsananta tsakanin bangarorin biyu.

 

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet